Labarai
Limamin Jumu’a ya caccaki mabarata
Limamin masallacin Juma’a na marigayi Sunusi Dantata dake Kofar Ruwa, Sheikh Muhammad Nuru Muhammad, ya ce, dabi’ar barace-barace da yara almajirai da kuma masu matattar zuciya ke yi, ba dabi’a bace mai kyau, asalima addinin musulunci ya yi hani da irin wannan halin a cikin al’umma.
Sheikh Muhammad ya bayyana hakan ne a cikin shirin Duniyar Mu A Yau na nan gidan Freedom Rediyo, da ya maida hankali kan batun hana bara a titunan jihar Kano.
Ya ce, batun hana bara a titunan jihar nan ga almajirai da ma wasu mutane, sai gwamnati ta yi kokari sosai wajan ganin anyiwa makarantun AlQur’ani hidima kamar yadda a ka yiwa makarantun boko ta hanyar gina guraren karatu tare da daukar nauyin kwararrun malamai.
Sheikh Muhammad ya ce, lokacin da turawan mulkin mallaka su ka zo Najeriya, sun bi gari-gari da kauyuka lungu da sakon kasar nan don samar da gine-ginen makarantun boko da malamai domin bada ilimin kyauta amma sai sukayi shakulatin bangaro da makarantun Islamiyyu.
Karin labarai:
Ganduje zai fara gurfanar da iyayen almajirai masu bara a gaban kotu
Gwamnatin Jihar Kano zata hana mata bara
Haka shima tsohon shugaban kungiyar kishin al’ummar jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi da ya kasance cikin shirin, ya ce, sunyi ta kokari wajen ganin an zartar da dokar kare hakkin kananan yara da kuma hana bara da gwamnatin jihar Kano ta kafa.
Shugaban ya kara da cewa, ya kamata gwamnati ta tilastawa iyayen yara wajen daukar dawainiyar yaransu kamar yadda addinin musulunci ya tanada don samun ingantacciyar tarbirya.
Bakin sunyi kira ga gwamnati kan dokar tallafawa makarantu AlQur’ani da ta mika al’amuran ga hannun hukumar AlQur’ani da makarantun Islamiyyu domin magance matsalar a fadin jihar baki daya.
You must be logged in to post a comment Login