Manyan Labarai
Gwamnatin Jihar Kano zata hana mata bara
Gwamnatin jihar Kano tace zata fito da wasu tsare tsare da zata hana mata barace barace a titunan jihar Kano.
Daraktar kula da harkokin mata a ma’aikatar mata ta jihar Kano Hajiya Kubra Dankani ce ta bayyana hakan lokacin da take tattaunawa da filin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio .
Hajiya Kubra tace barace baracen da mata ke yi a wasu titunan jihar Kano abu ne na damuwa wanda ya hada da sakacin mazajen su.
Tace duk da wannan halaye da mata suka shiga a jihar Kano ma’aikatar kula da walwalar matar ta jihar Kano na fito da tsare tsare da suke taimakawa mata a fadin jihar Kano.
Ministar harkokin mata Aisha Jummai Alhassan ta yi murabus daga mukamin ta
Matasa sun yi zanga-zanga kan aikin Titin Five Kilometer
Tace maaikatar mata ta hanyar ofishinta na bawa mata marasa karfi tallafi na sana’oi da suke aiwatarwa da sauran su.
Hajiya Kubra ta kara da cewa bayan tallafi da suke bawa mata ,tace matan da suka rasa mazajansu ko ta hanyar guduwa maaikatar na biya musu kudaden haya idan akayi bincike kuma aka tabbatar gaskiya ne.
Hajiya Kubra Dankani tace gwamnatin jihar Kano ta damu matuka a game da barace baracen da mata ke yi akan titunan jihar Kano musamman ma da daddare.