Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Limamin Kano ya bukaci al’umma su rinka yiwa shugabanni addu’a

Published

on

Limamin Kano Farfesa Sani Zahraddin ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da yin adduar samun dauwamammen zaman lafiya a Jihar Kano da ma kasar nan baki-daya.

Farfesa Sani Zahraddin ya bayyana hakan ne da safiyar yau yayin gudanar da taron addu’ar cikar tsohon sarkin Kano Marigayi Alhaji Ado Bayero shekaru 6 da rasuwa.

Ya kuma kara da cewa wajibi ne jama’a su rinka yi wa shugabanni addu’ar neman jagorancin ubangiji a cikin harkokinsu.

Sarkin Kano ya bude masallacin juma’a na sabuwar jami’ar Bayero

Yakamata a’lumma su siffanta da dabi’ar kunya-Limamin Zam-zam

Da ya ke jawabi yayin taron addu’ar gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje addu’a ya yi ga marigayin tare da fatan All.. ya ci gaba da karfafa bayansa.

A na sa bangaren sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, gode wa malamai ya yi bisa ga adduo’in da suke yi na kariyar annobar Corona, tare da yin addu’ar nemawa mahaifinsa da sauran magabata rahamar ubangiji.

Wakiliyarmu Zahra’u Nasir ta rawaito cewa malamai da dama ne suka yi ta gudanar da addu’o’in a yayin taron.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!