Connect with us

Labarai

COVID-19: Ma’aikata za su koma aiki a Katsina

Published

on

Bayan daukar tsawon makonni ana zaman lockdown a jihar ta Katsina tun bayan da aka samu bullar cutar Covid-19, yanzu haka dai gwamnatin jihar ta umarci dukkanin ma’aikatan jihar kama daga matakin kananan hukumomi zuwa jiha, da su koma bakin aiki.

A wata sanarwa da gwamna Aminu Bello Masari ya fitar, gwamnatin ta kuma bude dukkanin kasuwannin jihar, bayan da aka samu raguwar masu dauke da cutar ta Covid-19 a fadin jihar.

Wani dan kasuwa mai suna Alhaji Mamman Mai-Wake yace sun ji dadin wannan mataki da gwamnatin jihar ta dauka, la’akari da yadda suka fuskanci wani yanayi na matsi sakamakon zaman gida dole a jihar.

“Munji dadin wannan al’amari sosai, musamman mutanen da suke takure a gida sakamakon rashin harkokin kasuwanci” in ji shi.

Rahotanni sun ce da dama daga cikin ‘yan kasuwar da suka dogara da iya kasuwanci sun shiga halin ni ‘ya su sakamakon rashin samun kudaden shiga, yaynayin da harkokin kasuwanci suka tsaya cak.

Lokacin da cutar Coronavirus ta yi ‘kamari a jihar Katsina ne gwamnatin jihar ta bayar da umarnin rufe manyan kasuwannin jihar irin su Mashi, Dandume, Bakori da Jibiya  da Mai-Aduwa, Jibiya, Kafur da Kankara da sauran kasuwannin da ke ci a kowanne mako.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 331,789 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!