Labarai
Lionel Messi ya amince da kwantiragin shekaru biyu a PSG

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Lionel Messi ya cimma yarjejeniyar kwantiragin shekara biyu da PSG.
A yanzu haka dai Messi ya sauka a babban birnin Faransa domin kammala sanya hannu a kwantiragin nasa.
PSG ta amince zata rinka biyan Messi jimillar kudi Yuro miliyan 35 a kowace shekara.
Kwantiragin zai kare ne a karshen kakar wasa ta shekarar 2023 tare da zabin karin shekara guda.
You must be logged in to post a comment Login