Labarai
Ronaldo ya amince da ci gaba da zama a Saudi Pro League

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr Cristiano Ronaldo ya shirya ci gaba da zama a kungiyar inda ya ke fatan buga gasar kofin Duniya na shekarar 2026 da ke tafe.
Cristiano Ronaldo dai, ya amince da ci gaba da zama a gasar Saudi Pro League nan da shekaru biyu masu zuwa.
Bayan shekara guda ta farko, shekara ta biyu za ta zama zabi ga dan wasan gwargwadon kokarin da kuma shirin sa.
Karin kwantiragin nasa zai bai wa gwarzon dan wasan duniyar har sau biyar damar zama a Riyadh zuwa 2026.
You must be logged in to post a comment Login