Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Lionel Messi ya lashe Ballon d’Or karo na 7

Published

on

Dan wasa Lionel Messi ya sake lashe kyautar Ballon d’Or karo na bakwai ta shekarar 2021.

Messi wanda ya zura kwallaye 41 da tai makawa aka zura kwallo 17 a wasanni 56 da ya buga a kungiyarsa da kuma kasarsa ta Argentina.

Cikin nasarar da dan wasan ya samu harda lashe gasar Copa America a karo na farko a tarihi.

A gasar da dan wasa Messi ya lashe ta Copa America din ya yi nasarar lashe Golden Ball da Golden Boot da hakan ya sa ya doke tarihin La Albiceleste dan kasar Brazil da ya taba lashewa a shekarar 1993.

A yanzu dai Messi, ya zura kwallaye hudu a wasanni tara a kungiyarsa ta Paris Saint-Germain da hakan ya tabbatar da shine gwarzan kyautar Ballon d’Or.

Bikin bada kyautarda tsohon dan wasan Chelsea Didier Drogba ya jagoranta a dakin taro na Theatre du Chatelet da ke birnin Fari na kasar Faransa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!