Labarai
Lokaci ya yi da manyan hafsoshin tsaron Najeriya za su fita bakin daga- Bulama Bukarti

Lauyan nan mai zaman kansa a Najeriya Barista Audu Bulama Bukarti ya bayyana cewa, lokaci ya yi da ya kamata dukkan hafsoshin tsaron Najeriya su tafi bakin daga domin kawo karshen matsalar tsaro a kasar.
Audu Bulama Bukarti ya bayyana haka ne lokacin da ya ke tattaunawa da DCL Hausa.
Ya ce kamata ya yi hafsoshin tsaron su dawo yankunan da ke fama da matsalolin tsaro na din din din har sai sun magance matsalolin ta’addanci,
Bukarti ya kuma ce kamata ya yi Tinubu ya fito da dokoki na yiwa matsalolin tsaro garanbawul kamar yadda ya yi wa haraji.
You must be logged in to post a comment Login