Labarai
Lokaci ya yi da za mu tashi tsaye wajen kare yankunanmu na Arewa- ACF

Kungiyar Tuntuba ta Dattawan Arewa (Arewa Consultative Forum – ACF) ta yi kira ga gwamnonin jihohi 19 na Arewa da su gudanar da cikakken sauyi a tsarin mallakar ƙasa, domin dakile yunkurin wasu baƙi na kwace yankunan Arewa.
Shugaban kwamitin amintattu na ACF, Alhaji Bashir Dalhatu Wazirin Dutse ne ya bayyana hakan a yayin wani taro da aka gudanar a jihar Kaduna.
Ya ce abin takaici ne yadda ‘yan Arewa ke fuskantar ƙalubale wajen mallakar ƙasa a kudu yana mai nuna damuwa kan yadda wariya da kiyayya ke ƙaruwa a kudancin ƙasar nan kan ‘yan Arewa .
Ya kuma danganta hakan da wasu manufofi na rashin adalci da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa a yanzu da suka fi fifita kudu fiye da Arewa.
A cewarsa, lokaci ya yi da ya kamata gwamnonin Arewa da ‘yan majalisunsu su dauki mataki wajen gyara tsarin mallakar ƙasa domin kare muradun yankin.
Wazirin Dutse ya kuma bayyana cewa waɗannan abubuwa marasa daɗi na haddasa rashin jin daɗi da gamsuwa a zukatan mutane da dama daga Arewa.
You must be logged in to post a comment Login