Connect with us

Coronavirus

Lokacin buɗe makaranta bai yi ba – Boss Mustapha

Published

on

Gwamantin tarraya ta gargaɗi gwamnonin jihohi da kada su buɗe makarantun jihohinsu, har sai gwamnatin tarraya ta bada umarnin yin hakan.

Shugaban kwamitin karta-kwana na fadar shugaban ƙasa da ke yaƙi da cutar Corona kuma sakataren gwamnatin tarraya Boss Mustapaha ne ya bayyana hakan, a wani taro da ya gudana kan hanyoyin kaucewa cutar corona.

A cewar sa, ba daidai bane gwamnatocin jihohi su bude makarantu ba tare sahalewar ta ba, sannan su ƙara shiri kan yadda za su kare dalibai tare da malamasu.

Boss Mustapha ya kuma ce, lokacin buɗe makarantu bai yi ba, kuma gwamnatin tarraya tana gargaɗin gwamnonin jihohi da kada su karya dokar da ta bayar ta buɗe makarantu ba tare da sahalewar ta ba.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!