Labarai
Ma’aikatan da suka fi kwazo zamu karfafawa gwiwa – Lamin Sani
Ma’aikatar karamar hukumar Nassarawa ta ce zata cigaba da inganta walwala da jin dadin ma’aikatan ta.
Shugaban karamar hukumar Nassarawa Dr, Lamin Sani ya bayyana hakan lokacin da yake rabawa wasu ma’aikatan karamar tallafin kudi da ya tassama Naira miliyan guda.
Dr, Lamin Sani ya kuma yi kira ga ma’aikatan da su cigaba da rubanya kokarin su wajen ciyar da karamar hukumar gaba.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da jami’in yada labarai na karamar hukumar Hassan Muhammed ya sanya wa hannu cewa, karamar hukumar na yin duk mai yuwa wajen gudanar da ayyukan cigaba ga alummar yankin.
Shugaban karamar hukumar ya kara da cewar tallafin na daya daga cikin kudororin karamar hukumar na karfafawa ma’aikatan gwiwa don su dinga zuwa aiki akan lokaci wajen sauke nauyin da aka dora musu.
Da take jawabi daraktan dake kula da harkokin ma’aikata Hajiya Umma Abbas godewa shugaban karamar hukumar ta yi bisa wannan tallafin ya yin da ta bukaci ma’aikatan karamar hukumar su cigaba da marawa shugabancin karamar ta Nassarawa baya wajen cimma kudirorin ta.
Da yake jawabi a madadin wadanda suka ci gajiyar tallafin Malam Ibrahim Muhammad bayyana farin cikin sa ya yi bisa wannan taimakon ya yin da ya yi alkawarin dorawa wajen cigaban karamar hukumar.
You must be logged in to post a comment Login