Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zamu gina shaguna don cigaban Dakata -Lamin Sani Kawaji

Published

on

Shugaban karamar hukumar Nassarawa Alhaji Lamin Sani, yace karamar hukumar zata cigaba da aikin data dauko na gina shaguna  a layin Sarauniya dake unguwar Dakata.

Hakan ya biyo bayan dambarwar zargin karamar hukumar da yin aikin ba bisa ka’ida ba, wanda al’ummar yankin da dama suka nuna adawar su da yin aikin kasancewar zai gurbata muhallin su duba da yadda tsarin ginin zai tsuke layin da ta’azzara matsalar data addabi layin shekara da shekaru na magudanar Ruwa.

Alhaji Lamin Sani, ya bayyana haka ne a ofishin sa, a lokacin daya ke zantawa da wakilan jama’ar unguwar da suka kai kukan su tare da korafin aikin don nemo bakin zaren aikin.

Labarai masu alaka.

Al’ummar Dakata sun koka akan ginin shaguna bisa magudanar ruwa

An dakatar da gasar Firimiyar kasar Ingila sabo da-Corona

Lamin Sani,ya ce  hukuma nada hurumin yin aiyyukan da ta ke so, na cigaba da bunkasa yankuna ,kasancewar ita take da iko da duk wasu filaye dake karkashin ikonta, ko jama’a na so ko akasin haka matukar aikin bai saba ka’ida ba, kuma zai amfani al’ummar yankin da kawo musu cigaba.

Al’umma da dama na unguwar sun soki lamarin tare da barranta kansu da wakilcin wanda suka zauna da shugaban karamar hukumar, da ayyana cewar ba da yawun su ba.

inda suka kara dacewa in har hukumar ta dau niyyar yin aiki na bunkasa yankin, sun fi bukatar gina musu Islamiyya a wajen da ake takaddama ba wai ginin shaguna ba.

Haka zalika, jama’ar yankin sun sha  alwashin bin hanyoyin da suka dace don ganin cewar ba ayi amfani da karfin mulki ba ,wajen shiga hakkin su da yancin su  ta hanyar yin ginin , a matsayin su na ‘yan kasa masu ‘yanci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!