Labarai
Ma’aikatan hukumar samar da ruwa ta jihar Kano sun jingine yajin aiki
Ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano, sun jingine yajin aiki da suka shiga daga ranar Talata, sakamakon zargin da suka yi na gaza fara basu sabon tsarin mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 71,000, da kuma wasu zarge-zarge.
Sakataren ƙungiyar ma’aikatan Muntari Ado Tattarawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai, yana mai cewa ce sun janye yajin aikin ne a yau Alhamis, sakamakon zaman da suka yi da babban sakataren ma’aikatar ruwa, da shugaban ma’aikatan jihar Kano, da kuma shugabancin ƙungiyar ƙwadago ta ma’aikatan hukumar da wasu ɓangarori.
Ya kuma ce za su koma teburin sulhu domin ci gaba da tattaunawa don neman nasarorin da ake nema, domin kamo bakin zare kan matsalolin da suke fuskanta.
A ranar Talatar da ta gabata ne dai ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano, suka tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.
You must be logged in to post a comment Login