Labarai
Borno: Ma’aikatan ƙananan hukumomi sun yi zanga-zangar lumana

Ma’aikatan ƙananan hukumomi a jihar Borno sun gudanar da zanga-zanga a Maiduguri don nuna rashin jin daɗinsu kan rashin aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 da aka amince da shi a Najeriya.
Shugaban kungiyar kwadago na jihar, Yusuf Inuwa, ya ce ma’aikatan ƙananan hukumomi ne suka fi fuskantar matsin rayuwa saboda hauhawar farashin kaya, inda ya bayyana cewa albashinsu ba ya isa ko na mako ɗaya.
Ya kuma ce duk da gwamnati ta fara biyan wasu rukuni kamar malamai da ma’aikatan lafiya, yawancin ma’aikatan ƙananan hukumomi har yanzu ba su shiga tsarin sabon albashin ba.
A baya, gwamnatin jihar Borno ta bayyana cewa akwai ƙalubale wajen aiwatar da sabon albashin saboda yawan ma’aikata a ƙananan hukumomi, inda aka ce kusan ma’aikata 90,000 ne ke aiki a ƙananan hukumomi 27 na jihar.
Gwamnatin ta ce wasu ƙananan hukumomi suna samun kasa da Naira miliyan 700 a wata, alhali suna buƙatar sama da Naira miliyan 778 don biyan sabon albashin, lamarin da ke haifar da matsala wajen aiwatar da tsarin.
You must be logged in to post a comment Login