Rahotonni
Ma’aikatan kamfanin Roda sun gudanar da zanga-zanga a Kano
Ma’aikatan Kamfanin S. Roda and Sons Nigeria Limited dake unguwar tukuntawa, a karamar hukumar birni sun koka dangane da rashin adalcin da aka musu a kamfanim.
Ma’akatan dai sun ce kudin da ake basu, sun-taka-kara-sun-karya ba, sannan ba’a basu alawus a yayin da sukayi aikin daya can-canci a basu, inda wasu suka ce ko matsalar data danganci lafiya ce ta samesu, kamfanin baya basu wani tallafi.
Wakiliyarmu Shamsiyya Farouk Bello ta rawaito cewa, da safiyar yau ne ma’aikatan kamfanin na S Roda suka yiwa gidan radio Freerom tsinke, wadanda suka zo da korafe-korafe kan kamfanin nasu.
Ma’aikatan sun ce shugabanin kamfani basa basu albashi yadda ya kamata, bare ayi maganar alawus, wanda suka ce hakan bai hanasu aiko ba dare ba rana.
Wasun su kuwa sun bayyana cewa duk lokacin da sukayi fashi, tofa sai an linka kudin aikinsu na kwanaki 3 an cire a cikin albashinka, wanda a yayin daka kara lokaci kana aikin ko kwana kayi, bazaa kara maka ko sisi ba.
Babban jami’in da yake kula da ma’aikata na Kamfanin S Rauda And sons, Auwal Musa ya bayyana cewa wannan korafin da ma’aikatan suka kawo ba haka yake ba, a cewarsa duk bukatun ma’aikatan suna kokarin suga sun biya.
Al’umma dai na ganin ya kamata gwamnati tasa ido, dangane da irin wadanan shakulatun bangaro da shugabanin kamfanoni keyiwa ma’aikatan Jihar nan, don a samu a dakile rikon sakainar kashin da sukewa ma’aikatan.
You must be logged in to post a comment Login