Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

MA’AIKATAN KAN TITI NA TAKA MUHIMMIYAR RAWA WAJEN LALACEWAR KAYAN GWARI

Published

on

Shugaban kasuwargwari ta ƴankaba Alhaji Aminu Lawan Nagawo ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar talata 16 ga watan Janairun 2024

Alhaji Aminu Lawan Nagawo ya ce ya kamata jami’an tsaro su gane cewa kayan gwari ba irin sauran kaya bane, adan haka suyi duba da irin matsalar da kayan yake da shi.

Ya ƙara da cewa akan wata ƙaramar matsala sai kaga ma’aikatan sun tare motar kayan gwari akan titi har ta kwana ba su sake ta ba wanda hakan yake bayuwa da lalacewar kayan na su.

Nagawo ya kuma ce zasu samar da wata hanya da zasu zauna da shugabannin jami’an tsaron da suke zama akan hanya domin samin daidaito, kasancewar yadda ake samin yawaitar kama motocin su akan hanya.

Haka kuma Nagawo ya miƙa saƙon taya murna ga gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf bisa nasarar da ya samu a kotun ƙoli, inda ya buƙaci gwamnan da yayi duba da kasuwar tasu wajen samar musu da hanyoyin ci gaba da kuma inganta harkar kasuwar su musamman ga matasan kasuwar.

Ku kuma shugaban kasuwar yace kasuwar ta ƴankaba gwamnati bata taɓa samar musu da wani tallafi ba wanda zai samar musu da ci gaba, kasancewar duk wani tallafi da za’a bayar ana turawa ne ga masu noman shinkafa da alkama adan haka suke fatan wannan gwamnatin zata tallafa musu a ɓangarori daban-daban na cikin kasuwar.

Daga ƙarshe shugabannin kasuwar ya ƙara nuna goyon bayan su ga gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!