Labarai
Ma’aikatar shari’a ta Kano ta bukaci alkalai su kawo karshen cinkoso a gidaje gyaran hali

Ma’aikatar shari’a ta Kano ta bukaci alkalai da su kawo karshen cin koson mutane da ake samu a gidajen yarin jihar ta hanyar kammala shari’un da suka dade a gaban su.
Hakan na cikin sanarwar da mai magana da yawun ma’aikatar Malam Najib Lawan Danbazau ya fitar.
A cewar sanarwar wannan na zuwa ne bayan ziyarar da sabon kwamishinan Shari’a na Kano Barrister Abdulkarim Kabiru Maude, SAN yakai kotuna da ma’aikataun shari’a dan ganin halin da suke ciki.
Kwamishinan ya samu rakiyar babban Sakataren ma’aikatar Barrister Salisu Muhammad Tahir da manyan daraktocinta da kuma sauran ma’aikata.
Haka zalika sanarwar ta ce Kwamishinan ya kai ziyara, kotunan shari’a inda ya tattauna da Grand Khadi Hon. Tijjani Ibrahim Yakasai kan dalilin da ya sa ake samun tsaikon kawo karshen wasu shari’un wanda suke daukan lokaci ba a gamasu ba, inda yace ma’aikatar shari’ar za tai aiki kafada da kafada da kotunan wajen ganin am magance cinkosan mutanan da ake samu a gidajen yarin na Kano.
You must be logged in to post a comment Login