Labaran Wasanni
Ma’aikatar wasanni ta hada gwiwa da Microsoft don horar da matasa 36,000 a Najeriya
Ma’aikatar matasa da wasanni ta Najeriya za ta horar da matasa sama da dubu 36 ilimin fasahar zamani wato tare da hadin gwiwar kamfanin Microsoft.
Mataimakin ministan matasa da wasanni na kasa Kan harkokin yada labarai, Mista John-Joshua ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abuja.
Sanarwar ta kuma ce, za a gudanar da horon a cikin shekara guda mai zuwa ta 2022, karkashin sabon shirin kamfanin Microsoft mai taken: Fasahar Zamani Tare Da Sauya Mu’amala Don Cigaba.
Da yake jawabi yayin sanya hannu kan yarjejeniyar da aka kulla da Microsoft a Abuja, Ministan wasanni Sunday Dare, ya ce, ya yi farin ciki da kamfanin ya amince wajen hada gwiwa da ma’aikatar don horar da matasan Najeriya su samu ilimin fasahar zamani.
“Wannan yana da matukar mahimmanci a cikin babbar ajandar mu don daukaka samarin mu ta hanyar sama musu aikin yi ko kuma ilimin kasuwancin zamani domin dogaro da Kai,” in ji Dare.
You must be logged in to post a comment Login