Labarai
Ma’aunin rahoton Shugaba Buhari Kan tattalin arziki da tsaro
Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta ce ‘shugaba Muhamadu Buhari zai bar mulki a yayin da harkar tsaro da tattalin arzikin ƙasar nan suka inganta fiye da yadda ya same su a shekarar 2015, lokacin da ya hau karagar mulkin ƙasar’.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar Femi Adesina ne ya bayyana haka yayin wata hira da ya yi da gidan talbijin na Channels.
To ko wani kallo masana kewa batun?
Freedom Radio ta tuntubi Dakta Muhammad Amin Fagge, Masanin tattalin arziki daga jami’ar Dutsen jihar Jigawa yayi bayani Kan kallon da yake yiwa batun.
Wanda ya ce ‘tarihin ya nuna tun daga shekarar 1969 ba’a taba samun hauhawar farashi daya Kai kaso 12 da digo 7 a kasar ba irin yanzu’.
‘Idan aka koma bangaren ciwo bashi, gwamnatin data gabata tayi kokari wajen ganin ta rage bashin da ake bin kasar nan, Inda a gwamnatin da take mulki yanzu ba’a samu hakan ba, sai ma Kara lodawa kasar bashi da tayi, wanda suke ganin ba’ayiwa kasar nan wani abin azo a gani ba, ta yadda bashin zai biya kanshi’.
Dr Amin Fagge ya ce ‘wannan misalin dama wasu misalai da dama ya ishi al’umma su auna a mizani da maganar da fadar Shugaban kasar ta fitar’.
A don haka yake ganin mutane da kansu zasu yiwa kansu hisabi.
Rahoton: Ahmad Kano Idris
You must be logged in to post a comment Login