An Tashi Lafiya
Madubin Africa: Tarihin Sarauniyar Angola Anna Nzinga kashi na Farko
An haifi Anna Nzinga a shekara ta 1583 a Ndongo wadda ita ce kasar Angola a yanzu, sunan mahaifinta Ngola Kilombo Kia Kasenda, wanda shi ne Sarkin Masarautar Ndongo dake tsakiyar Afirka a wancan lokaci, sunan Mahaifiyar ta kuma Kengela ka Nkombe.
Lokacin da ɗan’uwan Anna, Mbandi, ya kori mahaifinsa, ya sa aka kashe ɗan Nzinga, sai ta gudu tare da mijinta zuwa Matamba.
Bayan korar mahaifinta da kuma guduwar ta zuwa Matamba Danuwanta Mbandi ya mulki Masarautar Ndongo na wani lokaci, Mulkinsa ya kasance na Kamakarya da zalunci.
A shekarar 1623, turawan mulkin mallaka na kasar Portugal suka mamayi kasar suka sauke Mbandi daga karagarsa, lamarin da ya sa ya nemi yaruwarsa Nzinga ta dawo domin tattaunawa Kan wata yarjejeniya da turawan kasar Fotigal game da Bautar da su da kuma mulkin mallaka da suka fara yi musu Bayan sauke shi.
Bayan muharawa Mai zafi tsakaninta da turawan Portugal din wadda a cikin ta ta nuna bajinta a karshe Nzinga ta yi nasara akan gwamnan Fotigal, Correa de Souza, inda aka cimma yarjejeniyar maida da ɗan’uwanta kan mulki, da kuma takaita cinikin mutanen Masarautar a matsayin bayi.
Masu sauraro a nan zamu dakata sai kuma wani makon Idan Allah ya nufa.
You must be logged in to post a comment Login