Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Siyasa

Mafi yawan jami’an Gwamnatin Kano suna tare da mu a ɓoye – APC G7

Published

on

Jam’iyyar APC tsagin Sanata Malam Shekarau ta ce, mafi yawan jami’an Gwamnatin Kano suna tare da ita a bayan fage.

Ɗaya daga cikin jagororin tsagin Alhaji Murtala Alasan Zainawa ne ya bayyana hakan, a zantawarsa da Freedom Radio.

Zainawa ya ce, kaso tamanin zuwa casa’in na muƙarraban Gwamna Ganduje suna tare da su, lokaci ne kawai zai bayyana hakan.

Ya ƙara da cewa G7 su ne waɗanda suka taimaka wa Ganduje har ya kafa Gwamnati.

“Mu ba zamu zuba ido ana yin ba daidai mu yi shiru ba, shi ya sa muka kawo G7 domin mu tsaftace jam’iyya” a cewarsa.

Alasan Zainawa ya ce, suna fatan za a shawo kan dambarwar cikin gidan da jam’iyyar ke fuskanta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!