Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Aubameyang ya shiga kundin tarihi a Barcelona bayan zura kwallo uku

Published

on

Dan wasa Pierre-Emerick Aubameyang ya zura kwallo uku a wasan da Barcelona tayi nasara da ci 4-1 akan Valencia.

Fafatawar da ta gudana a ranar Lahadi 20 ga Fabrairun 2022 a wasan gasar La Liga ta kasar Spain.

Nasarar zura kwallo uku da
Aubameyang yayi, ya bashi damar kasancewa dan wasa na biyu a Barcelona da ya zura kwallo sama da biyu a wasansa na farko a gasar La Liga.

Inda ya kamo tarihin dan wasa Francisco Trincão da  ya taba zura kwallo biyu a ragar Alavés a Fabarirun 2021.

Tsohon dan wasan Arsenal kafin barinsa birnin London na kasar Ingila ya zura kwallo hudu a wasa 14 da ya fafata a Arsenal.

Nasarar da Barcelona tayi akan Valencia da ci 4-1 ya bata damar komawa mataki na hudu da maki 42 a gasar ta La Liga.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!