Connect with us

Labarai

Magudin zabe : Za’a gurfanar da malaman jami’o’i a kotu kan da tafka magudi

Published

on

Kwamishinan  zabe na jihar Akwa Ibom Mr Mike Igini ya ce hukumar zabe ta tabbatar da zargin da ake yi wa wasu malaman jami’o’I 3 na da hannu dumu-dumu wajen aikata magudin zabe a babban zaben da aka yi a kasar nan.

Mr Mike Igini ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a shalkwatar hukumar dake Uyo ya ce sakamakon hakan hukumar ta kore jami’an daga aiki.

A cewar kwamishinan zaben nan bada jimawa ba za’a gurfanar da malaman jami’o’in a kotu.

Sai dai kwamishinan zaben bai Ambato sunayen malaman jami’o’in ba a ya yin da yake jawabin ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 332,921 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!