Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Mahaifin Messi zai tattauna da Bacerlona kan sauya sheka da dan wasan zai yi

Published

on

Tun daga lokacin da dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Bacerlona Lional Messi, ya bayyana aniyyar sa ta san barin kungiyar, inda kungiyoyin kwallon kafa daban-daban a turai suka dukufa wajen son daukan dan wasan dan asalin kasar Argentina.

A yau Laraba dai mahaifin Lionel Messi ya isa kasar ta Sufaniya domin tattaunawa da shugaban kungiyar ta Bacerlona Josep Maria Bartomeu kan yunkurin da dan wasan yake na son barin kungiyar a bana.

A kwai yuwuwar dai dan wasan Messi, mai shekara 33, ya koma kungiyar Manchester City inda tunima ya amince da tayin shekara biyar da ita.

Manchester City dai ta yiwa dan wasan Messi tayin £623m kuma zai kwashe shekaru uku a kungiyar kafin ya tafi Newyork City.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!