Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Neymar ya kamu da cutar Corona

Published

on

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint Germain Neymar Junior yana daya daga cikin ‘yan wasa uku na kungiyar da suka kamu da cutar Corona, bayan wani gwaji da akaiwa yan wasan kungiyar.

Kungiyar kwallon kafar ta Paris Saint Germain ce ta tabbatar da hakan yau ta cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta.

Sanarwar ta kara da cewa ‘yan wasan zuwa yanzu na nan na karbar kulawar data dace bayan killace su da akai.

Ta kara da cewa gaba dayan ‘yan wasan kungiyar da masu horas da su za su ci gaba da zuwa domin gwada lafiyar su kan ko suna dauke da cutar.

Neymar dai kafin wasan karshe na cin kofin zakarun turai Champion League da kungiyar ta PSG ta je ya samu suka kan yuwuwar buga wasan na karshe sanadiyyar canjin riga da yai a wasan dab dana karshe da dan wasan kungiyar RB Lepzing ta kasar Jamus.

Wanda kuma daga baya aka tabbatar da dan wasan kan zai buga wasan na karshe.

Kungiyar kwallon kafa ta Paris Sent German dai itace ta samu nasarar lashe gasar cin kofin kasar ta Faransa wato gasar League 1, wadda aka dakatar da ita kafin kammalata sanadaiyyar Corona kuma aka tabbatar da kungiyar a matsayin wadda ta lashe gasar.

A ranar Litinin din data gabata dai kungiyar kwallon kafar ta PSG ta sanar da cewa ‘yan wasa biyu a kungiyar sun nuna alamun cutar ta Corona.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!