Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

NFF: Ma’aikatan ta sun kamu da COVID-19

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta kasa wato NFF ta tabbatar da ce wa mutane guda 4 daga cikin ma’aikatan ta sun kamu da cutar Corona.

Shugaban hukumar ta NFF, Amaju Pinnick ne ya bayyana haka, jim kadan bayan ya karbi sakamakon gwajin Coronavirus da aka yi wa ma’aikatan makwanni biyu baya.

Amaju Pinnick, ya ce, “Mun umarci a gudanar da gwajin cutar ga daukacin ma’aikatan hukumar, bayan da aka samu daya daga cikin manyan ma’aikatan dauke da cutar”.

Pinnick, ya kuma ce, “Mutun daya daga cikin wadanda suka kamu da cutar ya warke, ya yin da ma’aikatan lafiya ke ci gaba da kula da sauran karkashin kulawar hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasa NCDC”.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!