Labarai
Mahmood Yakubu ya miƙa ragamar INEC ga May Agbamuche-Mbu

Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC mai barin gado Farfesa Mahmood Yakubu, ya miƙa ragamar shugabancin hukumar ga Misis May Agbamuche-Mbu, wadda za ta rike matsayin shugabar hukumar ta riƙon ƙwarya.
An gudanar da bikin mika ragamar ne a ranar Talata yayin taron da yake gudana tsakanin Farfesa Yakubu da kwamishinonin zaɓe na jihohi (RECs a shalkwatar hukumar da ke Abuja.
Misis Agbamuche-Mbu, wadda ita ce tsohuwar kwamishina mafi dadewa a hukumar, za ta kula da harkokin gudanarwa na INEC har sai an naɗa sabon shugaba.
Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa ya mika shugabancin hukumar a hukumance ga Misis Agbamuche-Mbu, tare da kira ga sauran kwamishinoni da daraktoci su ci gaba da bayar da goyon baya da haɗin kai kamar yadda suka yi masa.
Wannan sauyi dai ya zo ne a dai-dai lokacin da hukumar ke ci gaba da shirye-shiryen gudanar da wasu muhimman ayyukan zaɓe a faɗin ƙasar nan.
You must be logged in to post a comment Login