Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Mahukunta su kawo karshen kisan kiyashi a Najeriya – Sarkin Muslmai

Published

on

Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku, ya bukaci mahukunta da su gaggauta kawo karshen kisan kiyashin da ake yi wa wadanda basu-ji- ba- basu gani ba, a yankin Arewa maso gabashin kasar nan.

Muhammad Sa’ad Abubakar na III ya bayyana hakan ne yayin taron sarkunan gargajiya da ya gudana a jihar Kaduna.

Sarkin ya kuma buga misali da irin yanda ake kisan gilla ga wadanda basuji ba basu gani ba a kudancin jihar kaduna, inda ya ce wannan abin A l….. wadai ne, kamata yayi abar al’ummar kasar nan da cutar covid 19 wacce ta addabe su.

Muhammad Sa’ad Abubakar ya kuma bukaci gwamtain tarayya dana jihohi da su hada kai da jam’ian tsaron kasar nan dan ganin an yaki ayyukan bata gari a fadin kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!