Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu bada gudunmawa wajen yaki da rashin tsaro a Najeriya – SIC

Published

on

Wata kungiya da ke rajin tattara bayanan tsaro mai suna Such Light Initiatives ta ce za ta ci gaba da ba da gudunmawa wajen taimakawa jami’an tsaro bankado maboyar batagari a fadin jihar Kano.

Babban jami’in kungiyar, Malam Tijjani Lawan ne ya bayyana hakan, yayin wata ziyara da kungiyar ta kawo nan tashar Freedom Radio.

Ya ce, kungiyar tana taka rawa wajen binciko manya da kananan masu aikata laifuka a sassa daban-daban na jihar Kano.

Da ya ke mai da jawabi, mataimakin janar manaja na rukunin tashar Freedom Radio, Malam Adamu Isma’ila Garki, cewa yayi, aikin kungiyar aiki ne mai kyau duba da yanayin da ake ciki na rashin tsaro a kasar nan.

Malam Adamu Isma’ila Garki, ya kuma yi kira ga al’umma da su rika bijiro da irin wadannan kungiyoyi, domin kuwa, gwamnati ita kadai, ba za ta iya dakile matsalolin tsaro ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!