Kiwon Lafiya
Mai dakin shugaban kasa ta bude ofishin kwamitin aminatattu na ‘yan fansho a Abuja
Mai dakin shugaban kasa Aisha Buhari ta bude ofishin kwamitin amintattu na ‘yan fasnsho dake Abuja da aka sanya masa suna da SINOKI HOUSE dake babban birnin tarayya Abuja.
Ginin mai hawan bene7 hadin gwaiwa ne da kamfanin fansho na Sinoki system International Limited da aka kulla yarjejeniyar shekaru kuma ake tsammanin za’a sami kudaden shiga da ya kai fiye da Naira biliyan guda a cikin shekaru goman farko.
Gwamnan jihar Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje wanda ya sami wakilcin mataimakin sa Nasiru Yusuf ya ce gwamnatin Kano ta sake jadada kudirin ta na goyawa tare da tallafawa ‘yan fansho na jihar na.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da jamin’in labarai na ma’aikatar Faruk Ghali Masanawa ya sanya wa hannu cewa, Nasiru Yusuf Gwauna ya ce gwamnatin Kano ta kirkiru da kwamitoci 2 na biyan hakokin ‘yan fasnho don tabbatar da dorewar biyan su. Shugaban kwamitin Amintattaun ‘yan fasnho na jihar Kano Alhaji Sani Dawaki Gabasawa ya godewa gwamnati ya yi bisa wannan namijin kokarin don walwala da jin dadin ‘yan fasho na jihar Kano