Connect with us

Labarai

Mai damfarar mutane ya kai kansa hukumar EFCC

Published

on

Wani matashi da ake zargin cewa, mai damfarar mutane ne a fannin daukar aiki, Idris Adamu, ya kai kansa shalkwatar hukumar EFCC a jihar Gombe.

jami’in hulda da jama’a na hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja.

Oyewale ya bayyana cewa an yi wani abu mai kama da almara a shalkwatar hukumar EFCC na shiyyar Gombe, lokacin da matashin mai matsakaicin shekaru ya shiga harabar ofishin ya kai karar kan tare da bayyana irin laifukan da ya ke aikatawa na zambatar mutane.

Ya ce wanda ake zargin da kan sa ya bayyana cewa yana tsoron hukumar ta EFCC ne saboda irin laifukan da ya ke aikatawa.

Haka kuma, ya bayyana cewa, matashi Idris Adamu, ya shiga ofishin EFCC ne da misalin karfe 1:00 na rana, ya kuma bukaci ganin shugaban riko na shiyyar ko kuma mataimakin kwamandan EFCC DCE, Sa’ad Hanafi Sa’ad.

bayan ganin shugabannin ne ya bayyana musu cewa, A baya ya karbi kimanin naira miliyan 9 ta asusun ajiyarsa na banki daga wasu mutane daban-daban da sunan zai sama musu aikin yi a ma’aikatun gwamnatin tarayya wanda kuma karya ya shirya musu.

jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, matashinya kuma shaida wahukumar ta EFCC cewa, ya na jin tsoronta ne bisa laifukanda ya aikata, shi ya sa ya je domin bayyana mata tubansa.

Oyewale ya ce, mukaddashin daraktan shiyyar bayan ya saurari furucin nasa, ya gode masa da yin wannan tuba tare da bayar da umarnin a kai wanda ake zargin sashen bincike domin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!