Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mai horas da kungiyar Inter Milan ya ja kunen ‘yan wasa don samun nasara

Published

on

 

Mai horas da Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan Antonio Conte, yaja kunnnan yan wasan Kungiyar da suyi dukkan mai yuwuwa wajen ganin sun samu nasara a wasan karshe na cin kofin zakarun turai na Europa da za su buga yau da Sevilla.

Conte ya kuma ce babu abin da yake da Dadi da kuma zama tarihi sama dakaje wasan karshe a gasa kuma ka samu nasara a wasan.

Mai horar da Kungiyar ta Inter Milan Antonio Conte ya dai taba lashe kofin zakarun turai a Kungiyar sa ta Juventus lokacin yana Dan wasa, ya kuma tabayin rashin nasara a wasan karshe a kofin a shekarar 1994, Wanda yace a don haka yasan yadda nasara take da kuma rashinta.

Wannan dai shine karon farko da Kungiyar ta Inter Milan tazo wasan karshe a wata gasa cikin shekaru tara da suka gabata.

Sevilla dai da Kungiyar ta Inter Milan zatai wan na karshe da ita a gasar ta zakarun na turai na Europa Bata taba samun rashin nasara ba a wasan karshe da take zuwa a gasar, inda tazo sau biyar kuma duka ta dauka yanzu haka tazo wasan karshe karo Shida kuma inta dauka ta dauki kofin sau Shida.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!