Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hukumar kwallon kafa ta FIFA ta kara wa’adin dakatarwa ga Yves Jean-Bart

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA, ta Kara wa’adin watanni uku kan dakatarwar da taiwa shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar Haiti, Yves Jean-Bart, kan zargin da ake masa na yiwa Yar wasan kwallon kafar Mata ta kasar Fyade a sansanin daukan horon su.

Tun a ranar 25 ga watan mayun Daya gabata ne dai hukumar ta FIFA ta dakatar dashi daga shiga dukkanin wasu al’amuran wasanni na tsawon watanni uku inda yanzu lokacin ya cika hakan kuma ya sanya ta Kara wasu watanni ukun don ci gaba da gudanar da Bincike.

Sai dai Yves Jean-Bart tun a wancen lokacin ya musanta zargin da ake Masa na aikata lalata da yarwasan.

Tun a wancen lokacin dai hukumar ta FIFA ta dakatar da Mr. Jean-Bart daga shiga dukkanin wasu al’amuran wasanni har sai ta kammala gudanar da bincike a kansa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!