Labarai
Majalisa ta yanke hukuci ga masu laifi a shafukan sada zumunta
Majalisar dattawa ta sake gabatar da kudirin da ke neman gudanar da daurin shekaru uku ga duk wani mutum da aka kama shi ya aikata wani laifi a shafukan sada zumunta.
Haka kuma kudirin dokar ya kuma ce za a iya bukatar wanda aka Kaman da ya biya tarar naira dubu dari da hamsin ko kuma a hada mishi duka zuwa gidan yarin shekara uku da kuma biyan tarar naira dubu dari da hamsin.
Shekaru uku da suka gabata ne dai majalisar ta jingine dokar bayan da ta fuskanci tirjiya daga wajen al’ummar kasar nan da ke kallon lamarin a matsayin wata hanya ta take ‘yancin fadin albarkacin baki.
Majalisar datijjai ta fara tafka mahawara kan kasafin 2020
Majalisar dattawa ta amince da babban jojin Najeriya shari’a Ibrahim Tanko Muhammad
Majalisar dattawa ta amince a biya wasu kamfanoni kudaden tallafin mai
Abaya-bayan nan ne dai ministan yada labarai Alhaji Lai Muhammed ya bayana cewa gwamnatin tarayya za ta fara tsaftace yadda al’ummar kasar nan ke amfani da shafukan sada zumunta na zamani
Kudirin wanda ya tsallake karatu na farko ya kuma bukaci da a ci tarar kafafen yada labarai da aka kamasu da laifin yada labaran karya naira miliyan goma.