Labarai
Majalisar Dattijai Na Zargin Mai Rikon Hukumar EFCC Da Karya Doka
Majalisar Dattijai ta zargi mai rikon mukamin shugabancin hukumar EFCC Ibrahim Magu da karya doka, a yunkurin da hukumar ta yi na kama tsohon babban daraktan hukumar tsaro ta farin kaya DSS Mista Ita Ekpenyong, da takwaransa na hukumar leken asiri ta kasa NIA Mista Ayo oke.
Majalisar ta ce ba daidai bane EFCC ta gudanar da irin wannan aiki ba tare da neman izinin mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro Manjo-Janar Babagana Munguno mai ritaya da kuma shugaban kasar ba.
Sannan Majalisar ta gargadi EFCC cewa matukar ta kuduri aniyar gudanar da bincike ko kama wani daga cikin jami’an tsaron farin kaya DSS ko na leken asiri wato NIA to ya zama wajibi ta nemi izinin shugaban kasa, kamar yadda sashe na 4 na kundin dokar da ya samar da hukumar tsaro ta kasa.
A cikin watan Nuwamban bara ne dai aka yi zargin cewa an samu sa-in-sa tsakanin jami’an EFCC da na DSS da kuma na NIA sakamakon yunkurin EFCCn na kama tsoffin shugabannin hukumomin a Abuja.
Shugaban kwamitin Majalisar karkashin jagorancin Sanata Francis Alimikhena, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya binciki lamarin, sannan kuma ya ce za su gabatarwa Majalisar rahoton bincikensu da zarar Majalisar ta koma zamanta bayan hutun Easter.