Labarai
Majalisar dattawa ta amince da babban jojin Najeriya shari’a Ibrahim Tanko Muhammad
Majalisar dattawa ta amince da mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammed ya zama cikakken babban jojin Najeriya.
A ranar Alhamis da ta gabata ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikewa da majalisar ta dattawa da sunan mai rikon mukamin na babban joji, Ibrahim Tanko Muhammed, domin nadashi a matsayin cikakken babban jojin Najeriya.
Tun farko dai an nada Ibrahim Tanko Muhammed a matsayin mai rikon mukamin babban jojin Najeriya ne a watan Janairu, bayan da shugaba Buhari ya dakatar da mai shari’a Walter Samuel Onnoghen biyo bayan zargin sa da aka yi da kin bayyana wasu daga cikin kadarorin da ya mallaka.
A yayin zaman majalisar na jiya dai, mambobinta sun yi ta yi mishi tambayoyi wanda daga bisani suka amince da shi a matsayin cikakken babban jojin Najeriya.
An dai haifi mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammed a garin Doguwa da ke yankin karamar Hukumar Giade a jihar Bauchi, a ranar talatin da daya ga watan Disamban alif da dari tara da hamsin da uku.