Connect with us

Labarai

Hukumar lafiya ta bayyana yaduwar cutar Ebola a jamhuriyar Congo

Published

on

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta bayyana yaduwar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo a matsayin abin damuwa ga kasashen duniya.

Shugaban hukumar Tedros Adhanom Gebreyesus, ya ce, lokaci yayi da za a fadakar da duniya barazanar da cutar ke dauke da shi, kamar yadda kwamitin kwararru ya bada shawara akai.

Gebreyesus ya ce, duk da yake daukar matakin ba zai sauya asalin abinda ke faruwa a Congo ba, amma kuma zai bada damar sanar da duniya domin ganin an dauki matakan da suka dace na shawo kan cutar.

Wannan shine karo na farko da Hukumar ta dauki irin wannan mataki bayan irin wanda aka yiwa cutar murar tsintsaye a shekarar 2009 da polio a shekarar 2014 da Ebola a shekarar 2014 zuwa 2016 da kuma Zika a shekarar 2016.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!