Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar dattijai na yunkurin fitar da dokar siyawa jami’an sojin Najeriya sababbun makamai- Elisha Abbo

Published

on

Majalisar dattawa ta ce ta fara yunkurin samar da dokar da za ta bada damar fitar da kudaden da za’a siyawa jami’an sojin ruwan kasar nan sababbun makamai da za su taimaka musu a yunkurin da suke na samar da tsaro da inganta tattalin arzikin Najeriya.

Mataimakin kwamatin majalisar kan ayyukan rundunar, Sanata Elisha Abbo, dake wakiltar jihar Adamawa ta Arewa ne ya bayyan hakan yayin taron shekara na rundunar sojin ruwan kasar nan da take gudanarwa a nan Kano.

Zamu kara himma wajen ciyar da tattalin arzkin Najeriya gaba -Navy

Ya kuma ce sojojin ruwa na kan gaba wajen habbaka tattalin arzikin Najeriya, a domin haka majalisar ke kokarin fitar da dokar da za’a siya musu sababbun makamai da su da jami’an sojin sama da kuma na kasa.

Elisha Abbo ya kuma godewa shugaban rundunar sojin ruwan kasar nan Auwal Zubairu Gambo kan kokarin da yake na inganta ayyukan rundunar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!