Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zamu kara himma wajen ciyar da tattalin arzkin Najeriya gaba -Navy

Published

on

Rundunar sojin ruwan Najeriya ta ce za ta Kara himma wajen ciyar da tattalin arzkin Najeriya gaba.

Shugaban rundunar Auwal Zubairu Gambo, ne ya bayyana hakan yayin taron shekara na manyan hafsoshin sojin ruwan Najeriya da take gudanarwa a nan Kano.

Samar da sansanin sojin ruwa a Kano ci gaba ne -Navy

Taron da aka yi masa take da bunkasa tsaro a manyan tekunan Najeriya da zai Kara Samar da ci gaban tattalin arzkin kasar.

AZ Gambo, a jawabin nasa ya kuma ce rundunar za ta Kara inganta tsaro a manyan tekunan kasar domin ganin ta yi maganin mutanan dake safarar Manfetur a kasar ba bisa ka’ida ba.

Ya kuma godewa al’ummar Najeriya kan irin gudunmawar da suke bawa rundunar kan aikin da take na inganta tsaro.

Yau Alhamis 2 ga Satumbar shekarar 2021 aka shiga rana ta 3 da fara taron a nan Kano, inda kuma za’a Kwashe kwanaki 5 ana gudanar dashi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!