Labarai
Majalisar dattijai zata mikawa shugaba Buhari kunshin kasafin bana a Juma’ar nan
Majalisar dattijai ta ce a yau Juma’a ne zata mikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kunshin kasafin kudin bana da ta amince da shi a satin da ya gabata.
Shugaban majalisar dattijai Abubakar Bukola Saraki ne ya bayyana haka a jiya Alhamis yayin da yake jagorantar wasu daga cikin yan majalisar domin shan ruwa a fadar shugaban kasa.
Bukola Saraki ya ce an samu tsaikon gabatar da kasafin ne domin a tabbatar an tsefe shi gaba daya ba tare da samun wata matsala da zata iya bullowa a baya ba, bayan majalisun kasar nan sun sahale shi.
A ranar Larabar da ta gabata ne da ministan kasafin kudi da tsare-tsare Udoma Udo Udoma ya ce tsaikon da aka samu wajen mikawa shugaban kasa, zai kawo koma baya a harkar tattalin arzikin kasar nan.
A ranar 16 ga watan Mayun da muke ciki ne dai majalisun dokokin kasar nan suka amince da kasafin kudin, bayan ya shafe watanni shida a hannun su tun bayan da shugaban ya gabatar da kasafin a gaban zauren hadakar majalisar a watan Nuwambar bara.