Kiwon Lafiya
Majalisar dinkin duniya ta dakatar da ayyukan agaji a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Rann
Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da ayyukan agaji ga dubban ‘yan gudun hijirar da ke sansanin garin Rann a jihar Borno, a dalilin harin da mayakan Boko Haram suka kai kan barikin soji inda suka hallaka wasu jami’an agaji 3, wasu 3 kuma suka bace.
Sanarwar ta Majalisar dinkin duniya a Juma’ar da ta gabata, ta bayyana janye Jami ‘anta baki daya kimanin mutum 40 da ke ayyukan agaji a sansanin na Rann mai dauke da ‘yan gudun hijira akalla 55,000.
Haka zalika an dakatar da kai kayayyakin agaji zuwa sansanin na ‘yan gudun hijirar.
A daren ranar Juma’ar da ta gabata ne ita ma kungiyar Likitoci ta Najeriya Medecins sans Frontieres ta sanar da janye ayyukan ta a sansanin na Rann, sakamakon harin na mayakan Boko Haram.