Labarai
Majalisar dokoki ta Kano ta nemi goyan bayan masarautar Bichi
Majalisar dokoki ta jihar Kano, ta buƙaci masarautar Bichi da ta cigaba da baiwa majalisar haɗin kai wajen samun nasarar gudanar da ayyukan cigaban al’ umma.
Shugaban majalisar Engr Hamisu Ibrahim Chidari, ne ya bayyana hakan a yau Juma’a lokacin da shugabannin majalisar suka kai wa sarkin na Bichi ziyara a fadar sa.
Engr Hamisu Ibrahim Chidari, ya ce sun kai ziyarar ne da nufin gabatarwa masarautar sabbin shugabannin majalisar tare da neman hadin kanta domin yin ayyukan da za su ciyar da jihar Kano gaba.
A nasa ɓangaren, sarkin na Bichi Alhaji Nasir Ado Bayero, ya ce majalisar masarautar za ta ba su dukkan haɗin kan da ya dace, tare da buƙatar majalisar ta ƙara kaimi wajen yin dokokin da jihar Kano za ta amfana musamman ta fannonin ilimi da lafiya da sauran abubuwan more rayuwa.
Wakilinmu na majalisar dokokin Auwal Hassan Fagge, ya ruwaito cewa, shugaban majalisar ya kuma buƙaci al’umma da su kasance masu bin hanyoyin kariya daga cutar COVID-19 tare da yin addu’o’in ganin bayan Annobar.
You must be logged in to post a comment Login