Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano : Abubuwa bakwai da Ganduje ya fada akan Abduljabbar Nasiru Kabara

Published

on

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce daga yanzu ya fara daukar mataki kan kalaman batanci ga Annabi da  Abduljabbar Nasiru Kabara ya yi, tare da nuna isgilancin ga addinin musulunci.

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis  ya yin da yake jawabi ga malamai da limamai na jihar Kano dangane da kalaman da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ke yi na tunzura Jama’a akan fiyayyen halitta.

Abubuwa bakwai da Ganduje ya fada akan Abduljabbar Nasiru Kabara :
  1. Hudubar Limamai  ta mayar da hankali wajen  Kalaman batanci da  Abduljabbar Nasiru Kabara ya yi.
  2. Gwamnati ba zata zuba Ido tana ganin ana kalaman batanci ga fiyayyen halitta ba.
  3. Gwamna Ganduje ya ce “Wannan matakin yanzu ma mu ka fara dauka. Akwai abubuwan da za su biyo baya.”
  4. Da can mu na ta jin abubuwan da ake fada sai mu ka ce a kawo mana hujja akan hakan, “Mu na samun hujja sai mu ka dauki mataki kamar yadda a ka fara gani.”
  5. Ya kamata a kara nunawa al’umma munin wannan babban al’amari da Abduljabbar ke aikatawa.
  6. “Wannan hobbasa, ba ta gwamnati ba ce ita kadai. Ta mu ce gaba daya. Babban abin haushin ma shine, bayan karuwar faruwar irin wannan abu, sai ya zamana ma cewar abin ya na ma kara zurfi. Idan a ka yi la’akari da yadda wannan abin ya faru.”
  7. Sa’annan ya kara da cewa zai ci gaba da zama da Malaman saboda tuntubarsu kan yadda abin zai dinga tafiya. Ya kuma kara neman goyon bayan al’umma da ci gaba da yi wa jihar ta Kano addu’o’i kamar yadda a ka saba yi.

Abunda wasu malaman Kano suka ce kan matakin Ganduje :

Ka zalika wasu daga cikin malaman da suka yi jawabi a ya yin taron  sun ce ba sa bukatar Muqabala da wanda ya yi batunci ga Annabi Muhammad , Sallallahu Alaihi Wasallam.

Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, shugaban Izalatul Bid’ah Wa’ikamatussunnah na Kano, kuma Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Kano, cewa ya yi “Ba maganar wata mahawara da wanda ya zagi Annabin Tsira Sallallahu Alaihi Wasallam.”
Shi ma Shehi Shehi Maihula da Sayyadi Bashir Sheikh Tijjani Usman Zangon Barebari da Malamai da su ka yi magana a wajen, dukkansu sun hadu kan cewa ba bukatar zaman yin mahawara da duk mutumin da ya yi irin wadancan maganganu na batunci.

Sakon Mai alfarma sarkin Musulmi da Wazirin majalisar masarautar Katsina:

A jawabinsa na bude taro da takaitaccen bayani, Kwamishinan Harkokin Addini, Dr Muhammad Tahar Adam, ya bayyana irin sakonnin da su ke samu daga jama’a daban daban na yabawa da wannan mataki da gwamnatin jihar Kano ta dauka.

Ya ce, ”Sarkin Musulmi da Wazirin Katsina sun aiko da sakon jinjina ga Gwamna Ganduje kan matakin da ya dauka akan Abduljabbar Nasiru Kabara”.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!