Labarai
Majalisar dokoki ta tantance mutane 2 da za a naɗa su Kwamishinoni

Majalisar dokokin jihar Kano, ta kammala tantance mutane biyu da gwamnan Abba Kabir Yusuf, ya aike mata domin naɗa su muƙaman kwamishinoni.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya aike wa majalisar sunayen Dakta Aliyu Isa Aliyu da kuma da kuma Abdulkarim Rabi’u Maude SAN, domin neman sahalewar ta.
A zantawarsa da manema labarai bayan kammala tantance su Barista Abdulkarim Rabi’u Maude SAN, ya ce, yadda da amana ce ta sanya gwamnan aike wa da sunan sa domin ganin an naɗa su muƙamin na Kwamishina.
Shi ma da ya ke yin ƙarin haske bayan ya fito daga tantancewar, Dakta Aliyu Isa Aliyu, cewa ya yi, za su yi ƙoƙari wajen ganin sun sauke dukkanin nauyin da aka ɗora musu.
You must be logged in to post a comment Login