Ƙetare
Majalisar dokokin Isra’ila ta kaɗa ƙuri’ar samar da ƙudirin mallake gaɓar Kogin Jordan

Majalisar dokokin Isra’ila ta kaɗa ƙuri’a kan samar da ƙudirin mallake Gaɓar Yamma da Kogin Jordan a matsayin yankin Isra’ila.
Ƙudirin wanda wani ɗan majalisar mai tsattsauran ra’ayi ya gabatar na zuwa ne a dai-dai lokacin da Mataimakin Shugaban Amurka JD Vance ke ziyara a ƙasar domin tattauna batun tsagaita wuta a Gaza.
A watan da ya gabata, Shugaba Trump ya ce ba zai bari Isra’ila ta mamaye yankin ba, wanda Falasdinawa ke kallo a matsayin tasu kasar.
Sai dai Jam’iyyar Firaminista Benjamin Netanyahu ba ta amince da ƙudurin dokar ba, yayin da sauran mambobin gwamnatinsa suka amince da shi.
You must be logged in to post a comment Login