Connect with us

Labarai

Majalisar dokokin jihar Kano ta bukaci a kai wa mutanen Doguwa daukin gaggawa

Published

on

Ɗan Majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Doguwa Alhaji Salisu Ibrahim Muhammad ya bukaci gwamnatin jiha da ta tarayya da su gaggauta kai wa al’ummar garuruwan Tagwaye da Kusada da kuma Doka da ke ƙaramar hukumar da ya ke wakilta ɗauki sakamakon iftila’in ambaliyar ruwa da suka samu a yankin.

Alhaji Salisu Ibrahim Muhammad, ya yi wannan kira ne a yau yayin zantawarsa da manema labarai a zauren Majalisar biyo bayan irin halin da al’ummar yankin ke ciki na rashin muhalli a wannan lokaci sakamakon ambaliyar ruwa ga kuma damuna na shirin kankama.

Dan majalisar ya ƙara da cewa a matsayin sa da wakilin al’ummar wanɗannan yankuna, ya zama wajibi ya roki gwamnati domin ganin an kai musu ɗaukin gaggawa.

Dan majalisar ya sha alwashin ci gaba da shigewa al’ummar yankin gaba domin kai musu ɗauki a dukkannin ɓangarori na rayuwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!