Connect with us

Labarai

Majalisar Dokokin Kano na shirin bincikar shugabar Ƙaramar hukumar Tudun Wada

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano, ta sha al’washin gudanar da bincike kan ƙorafin da  wasu manoma ke yi  na zargin shugabancin ƙaramar hukumar Tudun Wada karkashin jagorancin Hajiya Sa’adatu Yusha’u, kan kwace musu gonakinsu da ke Dajin Gurfa a karamar hukumar ta  Tudun Wada a Kano. 

‎Shugaban masu rinjaye na Majalisar Alhaji Lawan Hussain Cediyar ƴan Gurasa ne ya tabbatar da hakan jim kaɗan bayan amsa gayyatar da Majalisar ta yi wa kungiyar da ke rajin kare hakkin Ɗan-adam da tabbatar da daidaito a cikin al’umma wadda ta aike wa Majalisar korafin Manoman.

‎‎

‎Da ya ke jawabi bayan amsa gayyatar da Majalisar ta yi musu, shugaban kungiyar Sa’id Bin Usman, ya ce akwai tarin korafe-korafe kan dambarwar hakkin mallaka na gonaki tsakanin shugabancin karamar hukumar Tudun Tada da kuma manoman yankin.

 

‎Manoma da dama ne a Dajin na Gurfa da ke yankin karamar hukumar Tudun Wada suka shigar da korafin su kan zargin  shugabar ƙaramar hukumar da ƙwace musu Gonakin su, in da kuma suke fatan majalisar dokokin jihar kano da ta duba kokensu domin samar musu da adalci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!