Labarai
Majalisar dokokin Kano na shirin samar da dokar koyar da kimiyya da fasaha cikin harshen Hausa

Majalisar dokokin Kano za ta samar da dokar da za ta bayar da dama wajen koyar da ilimin kimiyya da fasaha da harshen Uwa a makarantun jihar.
Dan majalisar mai wakiltar Takai Dakta Musa Ali Kachako, ne ya bukaci majalisar da ta kafa wannan doka da za ta tabbatar da koyar da kimiyya da fasaha a harshen uwa ga daliban Firamare da na ƙaramar Sakandire, bisa tanadin Manufar Harshen Kasa ta shekarar 2022.
Dakta Kachako, ya bayyana cewa koyar da darussa da harshen uwa zai taimaka wajen kara fahimtar dalibai da bunkasa sha’awar su ga karatu, musamman a fannoni kamar kimiyya da fasaha. Ya ce hakan kuma zai taimaka wajen kare al’adun harshen gida tare da kara inganta tsarin ilimi a matakin farko.
Mjalisar ta jaddada bukatar aiwatar da kudirin cikin gaggawa, domin inganta goge wa da kwarewar ɗalibai da kuma tabbatar da nasarar tsarin ilimi a jihar.
You must be logged in to post a comment Login