Labarai
Majalisar dokokin Kano ta amince da dokar kafa Rundunar tsaro mallakin gwamnatin jihar

Majalisar dokokin Kano ta amince da dokar kafa Rundunar tsaro mallakin gwamnatin jihar nan, bayan daukar tsawon lokaci ana dambarwa a majalisar kan sadarar dokar da yace ba’a yarda wanda yake rike da katin shaidar kowace jam’iyyar siyasa ba ya shugabanci Rundunar.
Majalisar ta amince da samar da dokar ne bayan shafe kusan fiye da tsawon awa daya ana muhawara akan da yawa daga cikin tanadin da dokar samar da Rundunar yayi kafin ayi mata karatu na uku.
Da yake Karin bayani akan kunshin dokar, Shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Husani Dala, ya ce sun yi cikakken Nazari da hangen nesa kafin yin dokar wadda zata taba kowane bangare na jihar Kano wajen daukar ma’aikatan ta musamman wadanda basu da alaka da harkar siyasa.
Dala ya kara da cewa Dokar da suka Samar ta amincewa jami’an Rundunar tsaron ta jihar nan su dauki kowane irin makami domin gudanar da ayyukan su, wanda ya hada da kamawa, hana aikata laifi da fatattakar masu aikata laifuka a fadin kano.
A dai zaman, majalisar ta amince da yin gyara akan dokar hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar nan da hukumar dake kula da sufuri a kwaryar birnin kano domin samun damar nada musu mataimakan shugabanni.
You must be logged in to post a comment Login