Labarai
Majalisar dokokin Kano ta amince da kara wa Kanotomomi watanni 3
Majalisar dokokin Kano ta umarci shugabannin Kantomomin ƙananan hukumomin jihar nan 44 da su je gaban komitocinta domin tantance su a Litinin mai zuwa.
Hakan dai ya biyo bayan amincewa da ƙara wa Kantomomin wa’adin watanni uku da zauren ya amince kamar yadda kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu kuma mataimakin gwamna Kwamared Aminu Abdussalam ya buƙata ta cikin wata wasiƙa da ya aike wa majalisar wadda shugabanta Alhaji Jibril Isma’il Falgore ya karanta yau.
Bayan karanta wasiƙar ne kuma shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Hussaini Chediyar ƴan Gurasa ya yi ƙarin haske da cewa bisa doka wa’adin kantomomin ya kusa karwewa, don haka gwamnatin Kano ke neman kara musu watanni uku.
You must be logged in to post a comment Login